-
Jami'an Tsaron Tunusiya Sun Kame Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Kasar
Oct 28, 2017 11:50Rundunar sojin Tunusiya ta sanar da kame wasu gungun 'yan ta'adda da suke shirye-shiryen kai hare-haren wuce gona da iri kan 'yan yawon shakatawa a lardunan kasar biyu.
-
Vladimir Putin: An 'Yantar Da Fiye Da Kashi 90 Na Kasar Siriya Daga Mamayar 'Yan Ta'adda
Oct 26, 2017 18:49Shugaban kasar Rasha ya tabbatar da batun cewa: An samu nasarar 'yantar da fiye da kashi 90 cikin dari na kasar Siriya daga mamayar kungiyoyin 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a cikin kasar ta Siriya.
-
Sojojin Iraki Sun Kaddamar Da Hare-Haren Kwato Yankin Kasar Na Karshe Da Ke Hannun ISIS
Oct 26, 2017 05:48Sojojin kasar Iraki sun sanar da fara kaddamar da wani gagarumin hari na soji da nufin kwato yankuna na karshe da suke hannun 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) a lardin Anbar na kasar.
-
Mayakan Kungiyar Yan Ta'adda Ta Daesh Sun Kai Hari A Kasar Libya
Oct 25, 2017 18:56Wasu majiyoyin sojojin kasar Libya sun bada labarin cewa mayakan kungiyan yan ta'adda ta Daesh sun kai farmaki kan wani barikin sojoji a garin Ajdabia daga gabacin kasar a yau Laraba.
-
Zarif Ga Tillerson: Masu Yakar kungiyar Da'esh Ba Sa Bukatar Izinin Wani
Oct 24, 2017 17:49Ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewar dakarun da suke fada da kungiyar ta'addancin nan ta Daesh (ISIS) ba sa bukatar izinin wani wajen kare kasarsu.
-
IS Ta Kashe Mutum 116 kafin Ta Arce Daga Tsakiyar Siriya
Oct 23, 2017 11:02Kungiyar kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriya ta ce kungiyar 'yan ta'addan IS ko Da'esh sun kashe fararen hula 116 kafin su arce daga yankin al-Qaryatayne.
-
Janar Baqeri: Daesh Suna Numfashinsu Na Karshe Ne A Kasar Siriya
Oct 20, 2017 17:16Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana cewar kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh tana numfashinta na karshe ne a kasar Siriya, yana mai jinjinawa irin nasarorin da aka ce ci gaba da samu a kan 'yan ta'adda a duk fadin kasar Siriyan.
-
Jami'an Tsaron Kasar Moroko Sun Kama Wasu Gungun 'Yan Ta'addan Kungiyar Da'ish
Oct 20, 2017 06:37Ma'aikatar harkokin cikin gidan Moroko ta sanar da kame wasu gungun 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da suke shirye-shiryen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri a kasar.
-
Sojin Siriya Sun Yi Wa Yankin Al-Mayadeen Kawanya
Oct 13, 2017 05:42Dakarun Sojin Siriya sunyi wa yankin Al-Mayadeen kawanya a wunkurin da suke na kwato yankin dake zaman sansani na karshe da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ke rike da a gabashin kasar.
-
Sojojin Syria Sun Rusa Wuraren Harba Makamai Masu Linzami Na 'Yan Ta'adda A Halab.
Oct 12, 2017 06:24Tashar telbijin din al'alam ta bada labarin cewa a jiya laraba ne sojojin na Syria sun kai harin ne a yankunan Lirmon da Rashidin da ke kusa da Halab.