IS Ta Kashe Mutum 116 kafin Ta Arce Daga Tsakiyar Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25134-is_ta_kashe_mutum_116_kafin_ta_arce_daga_tsakiyar_siriya
Kungiyar kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriya ta ce kungiyar 'yan ta'addan IS ko Da'esh sun kashe fararen hula 116 kafin su arce daga yankin al-Qaryatayne.
(last modified 2018-08-22T07:00:53+00:00 )
Oct 23, 2017 07:32 UTC
  • IS Ta Kashe Mutum 116 kafin Ta Arce Daga Tsakiyar Siriya

Kungiyar kare hakkin bil adama ta OSDH a Siriya ta ce kungiyar 'yan ta'addan IS ko Da'esh sun kashe fararen hula 116 kafin su arce daga yankin al-Qaryatayne.

Rahoton ya ce a tsawan kwanaki 20 da kungiyar ta yi kafin sojojin Siriya su kore ta daga yankin na al-Qaryatayne ta kashe fararen hula 116 a matsayin daukan fansa, a cewar shugaban kungiyar Rami Abdel Rahmane.

Kungiyar ta ce bayan kwace birnin dake yankin Homs an samu gawawarkin mutane da aka kashe da bindiga a kan tituna da gidaje da dai sauren wasu wurare.

Majiyoyin kungiyar ta OSDH sun ce an kashe mutanen ne a cikin kwanaki biyu da suka gabata, bisa zarginsu da fallasa bayanai ga sojojin gwamnatin Siriya.