Janar Baqeri: Daesh Suna Numfashinsu Na Karshe Ne A Kasar Siriya
(last modified Fri, 20 Oct 2017 17:16:21 GMT )
Oct 20, 2017 17:16 UTC
  • Janar Baqeri: Daesh Suna Numfashinsu Na Karshe Ne A Kasar Siriya

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Muhammad Baqeri ya bayyana cewar kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh tana numfashinta na karshe ne a kasar Siriya, yana mai jinjinawa irin nasarorin da aka ce ci gaba da samu a kan 'yan ta'adda a duk fadin kasar Siriyan.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya bayyana cewar Janar Muhammad Baqeri, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran, ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kai fagen daga a kusa da garin Aleppo na kasar Siriya a ci gaba da ziyarar da yake yi a kasar inda ya ce ko shakka babu karshen kungiyoyin ta'addanci yana daga kusatowa a kasar Siriyan.

Janar Baqeri ya ci gaba da cewa hadin kai da aiki tare da ake samu tsakanin sojojin Siriya da kawayenta da suke yaki a kasar a matsayin babban abin da ya taimaka wajen wannan nasarar da ake samu a kan 'yan ta'addan; yana mai bayyana fatansa na cewa dakarun Siriyan da kawayensu za su ci gaba da samun nasara a kan 'yan ta'addan.

A shekaran jiya Laraba ne dai babban hafsan hafsoshin sojojin kasar ta Iran ya fara ziyarar aiki a kasar Siriyan inda ya gana da manyan jami'an sojin kasar bugu da kari kan shugaban kasar Siriyan Bashar al-Asad inda suka tattauna kan ci gaba da hadin kai da aiki tare tsakanin kasashen biyu, kamar yadda kuma ya isar wa shugaba Asad din da wasikar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayydi Ali Khamenei ya aike masa.