-
Rawlings Ya Bukaci Trump Da Ya Kawo Karshen Kugen Yakin Da Yake Kadawa Kan Koriya Ta Arewa
Sep 27, 2017 16:33Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya kirayi shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya kawo karshen barazanar da yake yi na kai hari kasar Koriya ta Arewa yana mai cewa wajibi ne yayi hakuri da yanayin siyasar shugaban Koriya ta Arewan kamar yadda duniya ta yi hakuri da yadda yake gudanar da mulkinsa shi ma.
-
Jaridar Washington post Ta Bayyana Sabon Umarnin Shugaban Amurka Da Jahilci.!
Sep 26, 2017 19:21Jaridar ta Amurka ta ce; Umranin da shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya bayar na haka kasashe uku shiga cikin Amurka, nuna wariya ne mai hade da jahilci.
-
Shugaba Ruhani: Tattaunawa Da Amurka Bata Lokaci Ne Kawai
Sep 21, 2017 05:45Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya kore yiyuwar tattaunawa da Amurka yana mai cewa tattaunawa da ita bata lokaci ne kawai don kuwa ba ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ita.
-
Koriya Ta Arewa Ta Bayyana Barazanar Trump A Matsayin Wani Ihu Bayan Hari
Sep 21, 2017 05:45Ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewa, Ri Yong-ho, ya bayyana jawabin shugaban Amurka a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a matsayin wata alama ta wauta, yana mai cewa barazanar Trump ga Koriya ta Arewa wani ihu ne bayan hari.
-
Dr Ruhani: Amurka Tana Kaskanta Kanta Saboda Sabawa Ka'idojin Kasa Da Kasa
Sep 20, 2017 17:17Shugaban Hassan Ruhani na kasar Iran ya bayyana jawabin da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi a babban zauren majalisar dinkin duniya a jiya Talata da cewa, jawabin na trump ya kaskantar da kasar Amurka ne a gaban kasashen duniya.
-
Shugaban Kasar Amurka Ya Zargin Kasar Iran Da Goyon Bayan 'Yan Ta'adda
Sep 08, 2017 06:38A ci gaba da gudanar da bakar siyasarsa ta kiyayya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran; shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi kasar Iran da goyon bayan 'yan ta'adda a yankin gabas ta tsakiya.
-
Tashar CNN Ta Kamanta Trump Da Sarakunan Kama Karya
Aug 28, 2017 12:26Tashar talabijin ta CNN ta kasar Amurka, ta kamanta shugaban kasar Donald Trump da sarakauna masu mulkin kama karya.
-
Shugaban Venezuela Ya Jaddada Wajibcin Kara Karfin Kariyar Kasar Don Fuskantar Barazanar Amurka
Aug 25, 2017 16:36Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bukaci kwamandojin sojin kasar da su kara himma wajen kara karfin kare kai da kasar take da shi don fuskantar barazanar wuce gona da irin Amurka.
-
Taliban Ta Mayar Da Martani Ga Shirin Trump Na Aikawa Da Karin Sojoji Afghanistan
Aug 23, 2017 05:26Kungiyar ta'addancin nan ta Taliban ta kasar Afghanistan ta yi barazanar cewa za ta mayar da kasar ta zama makabarta ga sojojin Amurka matukar dai gwamnatin ta aiwatar da shirinta na ci gaba da mamaye kasar Afghanistan din.
-
Kasar Venezuela Ta Maida Martani Ga Barazanar Donald Trump
Aug 12, 2017 09:19Ma'aikatun tsaro da na harkokin wajen kasar Venezuela sun yi Allah wadai da barazanar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi wa kasarsu.