Shugaba Ruhani: Tattaunawa Da Amurka Bata Lokaci Ne Kawai
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya kore yiyuwar tattaunawa da Amurka yana mai cewa tattaunawa da ita bata lokaci ne kawai don kuwa ba ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ita.
Shugaba Ruhanin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a bayan fagen taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 72 da ke ci gaba da gudana a a helkwatar MDD da ke birnin New York, inda ya ce babu wata tattaunawa da za a yi da Amurka a daidai lokacin da Amurkan take magana kan ficewa daga cikin yarjejeniyar nukilyan da ake cimma da ita da wasu manyan kasashen duniya.
Shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da cewa: Mun dau shekaru muna tattaunawa da Amurka kan shirin nukiliyanmu, to amma a yau sai ga shi Amurkawa suna batun ficewa daga cikin yarjejeniyar. A saboda haka da wani dalili ne za a ci gaba da tattaunawa da Amurka a kan sauran batutuwa?
Shugaba Ruhanin dai ya ce Iran tana da wasu zabi da kuma matakan da za ta dauka matukar dai Amurka ta ki girmama wannan yarjejeniya.