Tashar CNN Ta Kamanta Trump Da Sarakunan Kama Karya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23614-tashar_cnn_ta_kamanta_trump_da_sarakunan_kama_karya
Tashar talabijin ta CNN ta kasar Amurka, ta kamanta shugaban kasar Donald Trump da sarakauna masu mulkin kama karya.
(last modified 2018-08-22T11:30:36+00:00 )
Aug 28, 2017 12:26 UTC
  • Tashar CNN Ta Kamanta Trump Da Sarakunan Kama Karya

Tashar talabijin ta CNN ta kasar Amurka, ta kamanta shugaban kasar Donald Trump da sarakauna masu mulkin kama karya.

A shafinta na yanar gizo, tashar CNN ta bayyana cewa, irin matakan da Trump ke dauka na neman tilasta jama'a bin ra'ayinsa a cikin kowane irin lamari, hali ne irin na sarakunan wasu kasashe masu mulkin kama karya.

Bayanin ya kara da cewa, a lokacin da Trump ya tafi hutu a kwanakin baya a jahar Arizona, ya yi wa 'yan jam'iyyarsa ta Republican barazana da cewa, idan ba su kada kuri'ar amincewa da daftarin kudirin da ke neman a gina katanga tsakanin Amurka da Mexico ba, to zai shiga kafar wando daya da su.

CNN ta ce masu sharhi da dama suna ganin cewa da irin wannan salo na siyasar Donald Trump, akwai yiwuwar jam'iyyarsa ta Republican ta fuskanci gagarumar matsala a zabe mai zuwa.