Jaridar Washington post Ta Bayyana Sabon Umarnin Shugaban Amurka Da Jahilci.!
Jaridar ta Amurka ta ce; Umranin da shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya bayar na haka kasashe uku shiga cikin Amurka, nuna wariya ne mai hade da jahilci.
Rahoton Jaridar 'Washington post" ya kuma kara da cewa;Sa'oi hudu kafin karewar wa'adin hana shigar mutanen kasashe 6 na musulmi cikin kasar ta Amurka, Fadar White House ta sake kara wasu kasashen uku a cikin wadanda aka hana shiga kasar.
Kasashen sune Korea ta Arewa, Venezuela, da Cuba.
A ranar litinin din da ta gabata, Donald Trump ya fitar da wani umarnin na hana mutanen kasashen Iran da Libya da Somaliya, Syria, Korea ta Arewa da Chadi da Yemen da Venezuela shiga cikin kasar.
A cikin watannin Janairu zuwa Maris ne shugaban na Amruka ya sanar da hana mutanen kasashen musuli 6 shiga cikin kasar, sai dai wata kotu a kasar ta bayyana hakan da cewa ya sabawa doka.