-
Tsohon Shugaban FBI: Donald Trump Makaryaci Ne
Jun 09, 2017 06:25Tsohon shugaban hukumar tsaro ta FBI a Amurka ya bayyana shugaban kasar Amurka Donald Trump da cewa mutum ne makaryaci.
-
Trump Ya Ce Larabawa Sun Sanar Da Shi Qatar Tana Goyon Bayan 'Yan Ta'adda
Jun 06, 2017 18:09Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar shugabannin Saudiyya da kawayenta sun bayyana masa cewar kasar Qatar tana taimakawa masu tsaurin ra'ayi na ta'addanci da kudade bayan da ya bukace su da kawo karshen taimakon kungiyoyin ta'addanci.
-
Nigeria Ta Nuna Damuwarta Kan Janyewar Amurka Daga Yarjejeniyar Paris
Jun 04, 2017 05:36Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi duk kuwa da ficewar da Amurka ta yi daga cikin yarjejeniyar wanda a cewar Nijeriya din hakan abin takaici ne.
-
Amurka Ta Fice Daga Yarjejjeniyar Dumamar Yanayi Na Paris
Jun 02, 2017 06:31Shugaban Kasar Amurka Donal Trump ya sanar da ficewar kasar sa daga yarjenniyar yanayi na birnin Paris tare da cewa babu Wani amfani da kasar sa ta samu a wannan yarjejjeniya.
-
Iran Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwagwarmayar Al'ummar Palasdinawa Domin Neman Yanci
May 30, 2017 06:57Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da nuna goyon bayanta ga al'ummar Palasdinu a gwagwarmayar da suke yi domin kai wa ga samun yanci daga bakin zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
S. Nasrallah: Saudiyya Ta Girmama Trump Ne Don Samun Goyon Bayan Yakar Iran
May 25, 2017 18:08Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana taron da Saudiyya ta shirya don maraba da shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin wani kokari na girmama Trump din da kada kugen yaki a kan kasar Iran da sauran kungiyoyin gwagwarmaya yana mai cewa hakan babu abin da zai kara musu face tsayin daka kan tafarkin da suke kai.
-
Dubban Mutane Suna Gudanar Da Zanga-Zangar La'antar Trump A Belgium
May 25, 2017 06:53Dubun-dubar jama'a ne suke gudanar da gangami da zanga-zanga a birnin Brussels da ma wasu biranan kasar Belgium, inda suke la'antar shugaban Amurka Donald Trump, tare da nuna rashin amincewarsu da zuwansa a kasarsu.
-
Kungiyar Tsaro Ta NATO Ta Bukaci Daukan Kwararan Matakan Yaki Da Kungiyar Da'ish
May 24, 2017 18:50Babban sakataren Kungiyar tsaro ta NATO ya bukaci daukan kwararan matakan yaki da Kungiyar ta'addanci ta Da'ish.
-
Sabon Kawancen Amurka, Saudiyyah, Isar'ila, Domin Yaki Da Iran
May 23, 2017 07:09Bayan gama ziyarar da ya kai a birnin Riyadh fadar masarautar Saudiyya, tare da gabatar da jawabi ga wasu shugabannin larabawa da na wasu kasashen musulmi, Donald Trump kai tsaye ya wuce zuwa Isra'ila.
-
Trump Da Salman Sun Ce Iran Ce Tushen Ta'addanci Na Duniya
May 21, 2017 17:20A taron da masarautar Saudiyyah ta shirya wa Donald Trump a birnin Riyadh wanda aka gayyaci wasu shugabannin kasashen larabawa da wasu na musulmi, sarkin masarautar Al Saud Salman bin Abdulaziz tare da babban bakonsa Donald Trump, sun dora alhakin dukkanin ayyukan ta'addancin da ke faruwa a duniya a kan kasar Iran.