Tsohon Shugaban FBI: Donald Trump Makaryaci Ne
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21158-tsohon_shugaban_fbi_donald_trump_makaryaci_ne
Tsohon shugaban hukumar tsaro ta FBI a Amurka ya bayyana shugaban kasar Amurka Donald Trump da cewa mutum ne makaryaci.
(last modified 2018-08-22T11:30:13+00:00 )
Jun 09, 2017 06:25 UTC
  • Tsohon Shugaban FBI: Donald Trump Makaryaci Ne

Tsohon shugaban hukumar tsaro ta FBI a Amurka ya bayyana shugaban kasar Amurka Donald Trump da cewa mutum ne makaryaci.

A lokacin da yake amsa tambayoyi jiya a gaban 'yan majalisar dokokin Amurka, tsohon shugaban hukumar ta FBI James Comey ya bayyana cewa, maganganun da Trump ya yi kan dalilan da suka sanya ya kore shi tsabar karya ya shirga.

Comey ya ce Trump ya bayyana cewa ya sallame shi saboda shi da hukumar FBI sun yi bincike a cikin wasikun Email na Hellary Clinton ne a lokacin yakin neman zabe, amma maganar gaskiya dalilin korarsa ita ce, binciken da FBI take gudanarwa gadan-gadan kan batun kutsen Rasha a cikin zaben Amurka ne, lamarin da zai iya jawo ma Trump gagarumar matsala, matukar binciken FBI ya tabbatar da gaskiyar abin da ake zargi, kan yadda Rasha ta yi wasan kura da zaben na Amurka.