Amurka Ta Fice Daga Yarjejjeniyar Dumamar Yanayi Na Paris
https://parstoday.ir/ha/news/world-i20934-amurka_ta_fice_daga_yarjejjeniyar_dumamar_yanayi_na_paris
Shugaban Kasar Amurka Donal Trump ya sanar da ficewar kasar sa daga yarjenniyar yanayi na birnin Paris tare da cewa babu Wani amfani da kasar sa ta samu a wannan yarjejjeniya.
(last modified 2018-08-22T07:00:11+00:00 )
Jun 02, 2017 02:01 UTC
  • Amurka Ta Fice Daga Yarjejjeniyar Dumamar Yanayi Na Paris

Shugaban Kasar Amurka Donal Trump ya sanar da ficewar kasar sa daga yarjenniyar yanayi na birnin Paris tare da cewa babu Wani amfani da kasar sa ta samu a wannan yarjejjeniya.

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa daga birnin Washington ya habarta cewa a jiya Alkhamis, Shugaban Kasar Amurka Donal Trump daga fadar White House ya sanar da ficewar kasar sa daga yarjejjeniyar yanayi da aka cimma a bornin Paris na kasar Faransa, tare da cewa za mi yi kokarin wajen sake kulla wata sabuwar yarjejjeniya da za ta amfani kasar Amurka.

Trump ya ce yarjejjeniyar Paris din  da aka cimma a baya za ta janyo hasara ga Al'ummar kasar Amurka, kuma sanadiyar cimma wannan yarjejjeniya Mutane da dama ne za su rasa ayyukan su musaman ma wadanda suke aiki a kamfononin kirar Motoci.

Saidai a bangare guda, kasashen Duniya sun yi alawadai da wannan mataki na Shugaba Trump , Firamin Ministar Birtaniya, Theresa May, ta shaida wa Shugaba Donad Trump takaicinta kan shawarar ficewa daga yarjjeniyar yanayin Paris da ya yanke, Shi ma shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce Faransa ba za ta sake kula wata sabuwar yarjejeniya kan yarjejeniyar ta baya ba, inda ya ce, zan shaida muku da kakkausar lafazi: ba za mu sake tattaunawa domin samun yarjejeniya mai karamar manufa ba ko ta yaya. A wannan Alkhamis, Faransa ta yi kira ga dukkan kasashen da suka rattaba hannu su tsaya kan yarjejeniyar Paris, kuma su kiyaye  nauyin da suka rataya wa kansu .

Ita ma Kungiyar tarayyar Turai ta ce ranar Alhamis wata ranar bakin ciki ce ga duniya, amma  ita za ta ci gaba da yakar dumamar yanayi domin tarihi na bayanta.