Nigeria Ta Nuna Damuwarta Kan Janyewar Amurka Daga Yarjejeniyar Paris
(last modified Sun, 04 Jun 2017 05:36:51 GMT )
Jun 04, 2017 05:36 UTC
  • Nigeria Ta Nuna Damuwarta Kan Janyewar Amurka Daga Yarjejeniyar Paris

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar Paris ta sauyin yanayi duk kuwa da ficewar da Amurka ta yi daga cikin yarjejeniyar wanda a cewar Nijeriya din hakan abin takaici ne.

Karamin minista a Ma'aikatar Muhalli ta Nijeriya din Ibrahim Usman Jibril ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar inda ya ce: Duk da cewa gwamnatin Amurka ta sanar da ficewarta daga yarjejeniyar ta Paris, to amma Nijeriya wacce ta sanya hannu kan yarjejeniyar a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar don kuwa hakan yayi daidai da maslaharta ne.

Kafin hakan ma dai wasu kafafen watsa labaran sun jiyo Ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya tana  cewa Nijeriya din kamar sauran kasashen duniya da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, za ta ci gaba aiwatar da alkawarin da ta dauka karkashin yarjejeniyar .

A ranar Alhamis din da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janye Amurkan daga cikin yarjejeniyar ta Paris da aka cimma ta a shekara ta 2015 bayan wani taro da shugabanni da wakilan kasashe kimanin 195 suka gudanar a birnin Paris babban birnin kasar Faransa dangane da yadda za a rage dumamar duniya. Shugabanni da 'yan siyasa da masana daga kasashe daban-daban na duniya na ci gaba da Allah wadai da wannan mataki da Donald Trump din ya dauka.