Pars Today
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya sha alwashin tabbatar da tsaron lafiyar al'ummar kasar, fada da rashawa da cin hanci da kuma kawo karshen fashi da makami da ke ci gaba da barazana ga tsaro da zaman lafiyan kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya jinjinawa kokarin da gwamnatin kasar Ghana take yi wajen fada da rashawa da cin hancin yana mai bayyana aniyarsa na hada kai da shugaban kasar wajen fada da wannan annoba da ta damu kasashen biyu.
Shuwagabannin Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) sun sha alwashin aiwatar da shirin kudi bai daya a tsakanin kasashen a shekara ta 2020 kamar yadda suka tsara
Ana shirin gudanar da wani zaman taron kara wa juna sani kan ayyuka da suka shafin bankin muslunci a kasar Ghana.
Gwamnatin kasar Ghana ta kulla yerjejeniyar hakar man fetur a cikin tekun kasar a yau Alhamis tare da kamfanin EXXO mobil
Kasar Ghana ta bayyana cewar ka kada kuri'ar rashin amincewa da matsayar Amurka na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila a yayin zaman babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ne don tabbatar da matsayar kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kuma kudururrukan Majalisar Dinkin Duniyan.
Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya kirayi shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya kawo karshen barazanar da yake yi na kai hari kasar Koriya ta Arewa yana mai cewa wajibi ne yayi hakuri da yanayin siyasar shugaban Koriya ta Arewan kamar yadda duniya ta yi hakuri da yadda yake gudanar da mulkinsa shi ma.
Jami'an 'Yan sanda a Ghana sun ce addadin mutanen da suka mutu a cikin wata mahakar zinari ta bayan fage a kudu maso yammacin kasar sun haura zuwa 22 daga 17.
Gwamnati za ta mika sha'anin tafiyar da makarantun addini ga wani bangare na musamman a kasar Ghana.
Mahukuntan Saudiyya sun dauki matakin tuso keyar wasu 'yan kasar Ghana su kimanin 5,00 wadanda ke rayuwa a kasar ba bisa ka'ida ba.