Za A Kirkiro Bangaren Kula Da Makarantun Addini A Kasar Ghana
Gwamnati za ta mika sha'anin tafiyar da makarantun addini ga wani bangare na musamman a kasar Ghana.
Ministan ilimi na kasar Ghana Matthew Opoku Prempeh ne ya bayyana hakan, inda ya ce an dauki wannan kudiri ne bayan kafa sabuwar gwamnati a kasar.
Ya ci gaba da cewa, makarantun addini suna daidai da sauran dukkanin bangarori masu matukar muhimmanci da suke bukatar gwamnati ta samar da yanayi mai kyau na kula da su.
A kan ya ce ma'iakatarsa za ta kirkiro wani bangare wanda zai rika zama mai tuntuba tsakaninsu da bangaren zartarwa.
Tun a cikin shekara ta 2014 majami'iun kiristoci suka bayar da shawar cewa ya kamata makarantun addini su zama suna cin gishin kansu ta fuskokin tsari da tafiyarwa, duk da cewa hakan ba zai hana gwamnati daukar nauyinsu ta fuskancin kudade ba, wannan shiri kuma zai hada da makarantun kiristoci da musulmi.