Zaman Taro Na Farko Kan Ayyukan Bankin Musulunci A Ghana
Feb 15, 2018 17:38 UTC
Ana shirin gudanar da wani zaman taron kara wa juna sani kan ayyuka da suka shafin bankin muslunci a kasar Ghana.
Rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya watsa ya bayyana cewa, za a gudanar da zaman taron kara wa juna sanin ne kan harkokin bankin musulunci a kasar ta Ghana a ranakun 25 da 26 ga watan Afirilun 2018, tare da halartar wakilai daga kasashen Malaysia, Singapore, Pakistan, Najeriya da kuma Iran.
Tsohon gwamnan babban bankin kasar Ghana shi ne zai jagoranci zaman taron, wanda zai gudana a cikin babban dakin taruka na jami’ar Ghana.
Haka nan kuma za a gabatar da makaloli kan batun bankin muslunci da kuma harkokin ajiyar kudi a musulunce.
Tags