Shugaban Kasar Ghana Yayi Alkawarin Kawo Karshen Fashi Da Makami A Kasar
Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya sha alwashin tabbatar da tsaron lafiyar al'ummar kasar, fada da rashawa da cin hanci da kuma kawo karshen fashi da makami da ke ci gaba da barazana ga tsaro da zaman lafiyan kasar.
Shugaba Nana Akufo-Addo ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi wajen bikin ranar da kasar Ghanan ta sami 'yancin kai da aka gudanar a birnin Accra inda ya ce: "Ina so in bayyana a fili cewa babu wani mutum da zai sami damar ci gaba da barazana ga rayuwar al'umma da kuma tabbatar da rashin tsaro a kasar Ghana" don haka sai ya kirayi jami'an tsaron kasar da suka hada da 'yan sanda da sojoji da su kara kai mi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan al'ummar kasar.
Yayin da ya koma kan batun rashawa da cin hanci kuma wanda yana daga cikin batutuwan da suke barazana ga tattalin arzikin kasar Ghanan, shugaba Nana Akufo Addo ya sake jaddada aniyarsa ta fada da wannan annobar yana mai cewa yanzu lokaci yayi da za a zage damtse wajen ciyar da kasar Ghanan gaba ta hanyar dogaro da dimbin arziki da albarkatun kasa da Allah Ya arzurta kasar.
Kalaman na shugaba Addo na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta shaidi wasu jerin fashi da makami da kashe-kashe a bangarori daban-daban na kasar lamarin da ya tada hankalin al'ummomin kasar.
Shekaru 61 da suka gabata a rana mai kamar ta yau 6 ga watan Maris ne dai kasar Ghanan ta sami 'yancin kanta daga turan mulkin mallakan Birtaniyya.