-
Jamia'n Tsaro Fiye Da 30,000 Ne Ke Gudanar Da Ayyukan Tsaro A Taron Arba'in A Karbala
Nov 14, 2016 08:02Babban kwamandan rundunar da ke kula da ayyukan tsaro na yankin Furat ya bayyana cewa fiye da jami’an tsaro dubu 30 ne za su gudanar da ayyukan tsaro a taron arba’in.
-
Sojojin Iraki Na Ci Gaba Da Kwace Yankunan Garin Mosil Daga Hannun 'Yan ISIS
Nov 12, 2016 16:49Majiyoyin sojin kasar Iraki sun bayyana cewar dakarun musamman na kasar da suke samun goyon bayan dakarun sa kai na kasar sun sami nasarar kwace wasu yankuna guda biyu a gabashin garin Mosul daga hannun 'yan kungiyar Da'esh (ISIS) a yau din nan Asabar bayan wani gagarumin gumurzu da ya gudana tsakanin bangarori biyun.
-
Sojojin Iraki Suna Ci gaba Da Samun Nasara A Mosel
Nov 12, 2016 12:02Sojojin Iraki Sun Kwace Yankin Arabjiyah da ke cikin Mosel.
-
Dakarun Iraki na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'addar IS a Mausil
Nov 09, 2016 11:22A ci gaba da kokarin tsarkake garin Mausil daga 'yan ta'addar IS, Dakarun sa kai na kasar Iraki sun tunkari sansanin Jiragen yaki na Tal'afar.
-
Mayakan Daesh Sun Sace Tsoffin Sojojin Kasar Iraqi 295 A Kusa Sa Birnin Musil
Nov 08, 2016 16:09Majiyar Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa mayakan kungiyar Daesh a birnin Musil na kasar Iraki sun yi garkuwa da tsoffin sojojin kasar kimani 295
-
Dakarun Iraki Sun Tsarkake Yankunan Gabashi Da Kudancin Mausul Daga ISIS
Nov 08, 2016 08:03Dakarun kasar Iraki suna ci gaba da nausawa zuwa yankunan da ke karkashin ikon 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS a Mausul da ke cikin lardin Nainawa a arewacin kasar Iraki.
-
Manufofin Hare-Haren Ta'addancin Baya-Bayan Nan A Kasar Iraki
Nov 08, 2016 05:48Rahotanni daga kasar Iraki sun bayyana cewar shugaban kasar Fu'ad Ma'asum ya sha alwashin cewa jinin mutanen da aka zubar sakamakon wani harin ta'addancin da aka kai garin Samarrah a kasar a ranar Lahadin da ta gabata ba zai tafi haka kawai ba tare da daukar fansa a kan 'yan ta'addan da suka kai harin ba; kamar yadda kuma ya kirayi hukumomin tsaron kasar da su dau matakan da suka dace wajen kawo karshen irin wadannan hare-haren ta'addanci.
-
Iraki: Fiye Da Mutane 10 Ne Su ka yi Shahada A Harin Ta'addanci A Garin Samarra.
Nov 07, 2016 06:30Harin Na jiya An Kai shi ne Da Mota Mai Makare Da Bama-bamai.
-
Haidar Abadi: Nan Ba Da Jimawa Ba Za'a Kwato Garin Mosil Daga Hannun Da'esh
Nov 06, 2016 17:35Firayi ministan kasar Iraki, Haider al-Abadi ya sha alwashin kawo karshen kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh da kuma kwace garin Mosil daga hannunsu a daidai lokacin da sojojin kasar Irakin da suke samun dauki dakarun sa kai na kasar suke ci gaba da kutsawa da nufin kwato garin na Mosil.
-
Badakalar Siyasa Tsakanin Masar Da Saudiyyah
Nov 06, 2016 06:05Sakamakon tabarbarewar da alakar diflomasiyya tsakanin Masar da Saudiyya ke fuskanta a cikin lokutan nan, hakan ya sanya Masar sake yin nazari dangane da farfado da alakarta da wasu kasashen da bata dasawa da su domin cike gibin abin ta rasa daga Saudiyyah.