Sojojin Iraki Suna Ci gaba Da Samun Nasara A Mosel
Nov 12, 2016 12:02 UTC
Sojojin Iraki Sun Kwace Yankin Arabjiyah da ke cikin Mosel.
Majiyar Sojan Iraki ta ce da safiyar yau asabar sun yi nasarar kame unguwar Arabjiyah da ke gabacin birnin Mosel.
Wani jami'in sojan Irakin Muntazar Salim ya shaida wa manema labaru cewa; wata rundunar sojan Irakin, tana kokarin datse hanyar da yan ta'addar Da'esh su ke samun taimako a tsakanin yammacin Mosel da Kasar syria.
Wata majiyar sojan Irakin ta ce, sojojin kasar sun yi nasarar kashe Abul-Walid al-Ansary daya daga cikin kwamandojin kungiyar ta Da'esh, tare da wasu 'yan ta'adda 9 da su ke a tare da shi,a yankin al-haurah, a arewacin birnin Bagadaza.
Tags