Dakarun Iraki Sun Tsarkake Yankunan Gabashi Da Kudancin Mausul Daga ISIS
Dakarun kasar Iraki suna ci gaba da nausawa zuwa yankunan da ke karkashin ikon 'yan ta'addan takfiriyyah na ISIS a Mausul da ke cikin lardin Nainawa a arewacin kasar Iraki.
Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoto daga yankin na Mausul cewa, dakarun kasar Iraki da suka hada da sojojin gwamnati da kuma sojojin sa kai, sun samu nasarar tsarkake yankuna da dama a gabashi da kuma kudancin Mausul, tare da halaka adadi mai yawa na 'yan ta'addan wahabiyawan takfiriyya na ISIS.
Rahoton ya ce a jiya ne dakarun suka kammala tsarkake kauyen Qabrul Abd mai tazarar kilo mita 5 daga filin safka da tashin jiragen sama na Mausul da ke hannun 'yan ta'adda.
Dakarun na Iraki sun ce sun samu nasarar yanke hanyar da ta hada Mausul da Raqqah da ke cikin kasar Syria, babbar hanyar da 'yan ta'addan ke samun taimako daga sauran takfiriyawa da kuma kasashen da ke daukar nauyinsu.