Badakalar Siyasa Tsakanin Masar Da Saudiyyah
Sakamakon tabarbarewar da alakar diflomasiyya tsakanin Masar da Saudiyya ke fuskanta a cikin lokutan nan, hakan ya sanya Masar sake yin nazari dangane da farfado da alakarta da wasu kasashen da bata dasawa da su domin cike gibin abin ta rasa daga Saudiyyah.
Jaridar Ra'ayul Yaum ta bayyana a cikin shafinta na yanar gizo cewa, a cikin wannan mako ministan mai na kasar Masar Tarik Mulla ya ziyarci birnin Bagadaza na kasar Iraki, inda ya gana da takwaransa na kasar Jabbar Al-lu'aibi, sun kuma tattauna muhimman batutuwa da suka shafi karfafa alaka a tsakanin kasashen biyu kan batun mai.
Wannan lamari bai zowa wa masu bin diddigin lamurra da mamaki ba, idan aka yi la'akari da yadda aka shiga kai ruwa rana a tsakanin Saudiyya da Masar a cikin 'yan makonnin da suka gabata, sakamakon amincewar da Masar ta yi da wani daftarin kudiri da Rasha ta gabatar a gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, wanda yake kira da a hada karfi da karfe tare da halastacciyar gwamnati a Syria wajen yaki da 'yan ta'adda a kasar, kudirin da Amurka, Faransa, Birtaniya tare da Saudiyya suka ki amincewa da shi.
Amincewa da wannan kudiri da Masar ta yi, ya jawo fushin Saudiyya a kanta, inda jim kadan bayan hakan Saudiyya ta sanar da yanke man fetur da take baiwa kasar Masar a kowane wata, tare da janye jakadanta daga birnin Alkahira, yayin da shi ma a nasa bangaren shugaban kasar ta Masar Abdulfattah Sisi ya mayar da martini kan lamarin da cewa, kasar Masar kasa ce mai 'yancin siyasa, kuma ita ce ke fayyace ma kanta abin da ya dace da ita, daidai da manufofin siyasarta.
Sai dai masana da dama suna ganin cewa Saudiyya za ta tafka babban kure matukar dai ta shiga takun saka da Masar, domin kuwa Masar ba daya take da 'yan kananan kasashen larabawa da Saudiyyah ke cin karenta babu babbaka a kansu ba, wanda kuma ga alama masu hangen nesa daga cikin masu rike da madafun iko a kasar ta Saudiyya sun hango hakan, inda suka tura tawaga zuwa Masar domin a tattauna lamarin kuma a kawo karshensa, amma ga dukkanin alamu Masar ta riga ta dauki wani matsayin na daban, inda ta aike da ministan mai zuwa Iraki domin neman ta maye gurbin man da take samu daga Saudiyyah da man kasar Iraki, haka nan kuma rahoton na jaridar Ra'ayul Yaum ya ce akwai wasu bayanan sirri da ke cewa ministan man na Masar ya mika wata wasika ga jami'an gwamnatin Iraki zuwa ga gwamnatin Iran, inda a halin yanzu Masar take bukatar ta kyautata alakarta da kasar Iran, kamar yadda kuma a halin yanzu gwamnatocin Masar da Syria suka kulla kawance na siyasa, wanda kuma zai hada da batun tsaro, lamarin da shi ma ko alama ba zai taba yi wa Saudiyya dadi ba.
Masana kan harkokin siyasa da dama sun yi imanin cewa, kawance tsakanin kasashen Masar, Iraki, Iran da kuma Syria, zai yi babban tasiri ta fuskar siyasa da tsaro a yankin gabas ta tsakiya baki daya, musamamn ganin cewa dukkanin wadannan kasashe suna dasawa da kasar Rasha, wanda ko shakka bubu hakan zai fayyace makomar lamurra a yankin, wanda a halin yanzu yake a matsayin zakaran gwajin dafi a kallon hadarin kajin da ake yi wa juna tsakanin kasashe biyu mafi karfi a duniya wato Rasha da Amurka.