-
Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai Afganistan
Apr 23, 2018 06:40Jamhuriya Musulinci ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajenta, Bahram Qasemi, ta yi allawadai da kakkausar murya da harin kunar bakin waken da aka kai a Kabul, babban birnin kasar Afganistan a jiya Lahadi.
-
Yarjejeniyar Nukiliya : Iran Za Ta Dawo Da Shirinta Na Nukiliya, Idan Amurka Ta Janye
Apr 22, 2018 06:46Ministan harkokin wajen Jamhuriya Musulinci ta Iran, Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta koma kan shirinta na nukiliya, idan har Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da ita.
-
Qasemi: Rahoton Amurka Kan Kare Hakkokin Bil Adama Batu Ne Na Siyasa
Apr 22, 2018 02:13Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana rahoton da Amurka ta fitar kan kare hakkokin bil adama a Iran da cewa magana ce ta siyasa kawai.
-
Zarif: Iran Za Ta Ci Gaba Da Shirinta Na Nukiliya, Matukar Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Nukiliya
Apr 21, 2018 01:14Ministan harkokin wajen kasar Iran, Dakta Muhammad Jawad Zarif, ya bayyana cewa Iran za ta sake dawowa da ci gaba da ayyukanta na nukiliya matukar dai shugaban Amurka ya sanar da ficewar Amurkan daga yarjejeniyar nukiliyan da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran din.
-
Limanin Juma'a Na Zanjan: Amurka Ba Za Ci Moriyar Yake-Yakenta A Gabas Ta Tsakiya Ba.
Apr 20, 2018 07:26Hijjatul Islam Ali Khatami Ya ce; Ko mai yawan kudaden da Amurka za ta kashe a yake-yaken da take yi a gabas ta tsakiya, ba zai haifar ma ta da mai ido ba.
-
Iran : Jagora Ya Daina Amfani Da Manhajar Telegram
Apr 18, 2018 13:30Shafin intarnet na adano da yada manufofin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya sanar da cewa Jagoran ya daina amfani da manhajar ''Telegram'' domin yin aiki da manhajojin sadarwa na zamani mallakin Iran, a matsayin martaba kasar.
-
Martanin Iran Kan Kasar Saudiya
Apr 18, 2018 03:21Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen Iran Bahram Qasemi ya yi watsi da zarge-zangen da sarkin saudiya ya yiwa Iran a taron kasashen larabawa karo na 29.
-
Shugaba Rauhani Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Sabon Shugaban Saliyo
Apr 18, 2018 02:10Shugaba Hassan Rauhani na Iran ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban kasar saliyo Julius Maada Bio.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Kame Wasu Nakiyoyi Da 'Yan Ta'adda Suka So Shigo Da Su Kasar
Apr 17, 2018 00:31Jami'an tsaron kasar Iran sun sami nasarar ganowa da kuma kame wani adadi mai yawa na abubuwa masu fashewa da 'yan ta'adda suka yi kokarin shigowa da su ta kan iyakar gabashin kasar.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Tarwatsa Wata Kungiyar Masu Fataucin Muggan Kwayoyi Ta Kasa Da Kasa
Apr 13, 2018 01:21Jami'an tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami nasarar tarwatsa wata kungiyar masu fataucin muggan kwayoyi ta kasa da kasa a gabashin lardin Kerman da ke kudancin kasar ta Iran.