-
Jagora Yayi Watsi Da Sanya Hizbullah Cikin Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Da Saudiyya Da Kawayenta Suka Yi
Apr 20, 2016 10:48Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga bayyana kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon da wasu kasashen larabawa, bisa matsin lamba da cin hancin da kasar Saudiyya ta ba su, suka yi a matsayin kungiyar ta'addanci yana mai cewa kungiyar Hizbullah dai ta kasance abar alfaharin duniyar musulmi.
-
Sabanin Iran da Saudiya riba ce ga Haramcecciyar kasar Isra'ila
Apr 20, 2016 04:27Shugaban Majalisar Fayyace tsarin milki na Iran ya ce Sabanin Kasashen Iran da Saudiya riba ce ga haramcecciyar kasar Isra'ila
-
Kasashen Musulmi Da Dama Ba Su Ji Dadin Bayanin Karshe Na Taron OIC A Istanbul Ba
Apr 19, 2016 15:19Kasashen musulmi da dama ba su amince da sakamakon zaman taron OIC da aka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya ba, musamman ma kan hankoron kasashen da ke juya taron na neman cin zarafin kasar Iran bisa dalilai na siyasa.
-
Iran Ta Ce Ba Za Ta Rage Yawan Man Fetur Da Take Fitarwa Ba
Apr 19, 2016 15:16Iran ta jaddada matsayinta na kin amincewa da da duk wani mataki na neman ta rage yawan man da take fitarwa zuwa kasuwanninsa na duniya.
-
Janar Pourdestan: Sojojin Iran Za Su Ci Gaba Da Ayyukan Da Aka Tura Su Yi A Siriya
Apr 18, 2016 05:21Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Iran Birgediya Janar Ahmad Ridha Pourdestan ya bayyana cewar sojojin Iran da suke kasar Siriya a matsayin masu ba wa sojojin kasar shawara za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a can a ci gaba da taimakon da suke ba wa sojojin a fadar da suke yi da 'yan ta'adda.
-
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gudanar Bikin Ranar Sojoji
Apr 17, 2016 17:50Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fuskar karfin soji baya barazana ga kasashen makobta da na musulmi.
-
Iran Ta Kauracewa Taron OPEC A Doha
Apr 17, 2016 10:27Kasashe masu arzikin man fetir na duniya na halartar wani taro a birnin Doha na kasar Qatar da nufin tattauna hanyoyin samar da wani tsari na bai daya domin farfado da farashin man daya fadi warwars a kasuwancin duniya.
-
An Cimma Yarjeniyoyi A Bangarori Daban-Daban Tsakanin Iran Da Tarayyar Turai
Apr 17, 2016 03:04A ziyarar da babbar jami'ar siyasar wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini take gudanarwa a Tehran, an cimma yarjeniyoyi a bangarori daban-daban tsakanin Iran da kuma kungiyar tarayyar turai.
-
Mogherini: Gwajin Makamai Masu Linzamin Iran, Bai Saba Wa Yarjejeniyar Nukiliya Ba
Apr 16, 2016 17:43Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta bayyana cewar gwajin makamai masu linzami da Iran ta yi a kwanakin baya bai saba wa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya ba.
-
Rouhani Yayin Ganawa Da Shugaban Senegal: Makiya Suna Kokarin Raba Kan Al'ummar Musulmi Ne
Apr 16, 2016 17:29Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana kokari rarraba kan al'ummar musulmi da kuma kirkiro kungiyoyi na 'yan ta'adda a matsayin wasu makirce-makirce guda biyu da makiya suke kulla wa al'ummar musulmi.