Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gudanar Bikin Ranar Sojoji
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i4009-jamhuriyar_musulunci_ta_iran_ta_gudanar_bikin_ranar_sojoji
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fuskar karfin soji baya barazana ga kasashen makobta da na musulmi.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 17, 2016 13:20 UTC
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gudanar Bikin Ranar Sojoji

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fuskar karfin soji baya barazana ga kasashen makobta da na musulmi.

A jawabin da ya gabatar a bikin ranar soji a yau Lahadi; Shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ya bayyana cewa; Rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana karkashin sanya idon da karbar umurni daga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ne bisa wasiyar marigayi Imam Khomeini {r.a} da ya assasa Jamhuriyar Musulunci a kasar ta Iran, don haka runduna ce ta Musulunci da suke kare manufofin addinin Islama da al'ummar kasa.

Sheikh Hasan Ruhani ya kara da cewa; Rundunar sojin Iran tana riko ne da koyarwar addinin Musulunci , don haka ta zame ni'ima ga al'ummar kasar ta hanyar kare tsaron kasa da manufofin al'ummarta.