Iran Ta Kauracewa Taron OPEC A Doha
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i4000-iran_ta_kauracewa_taron_opec_a_doha
Kasashe masu arzikin man fetir na duniya na halartar wani taro a birnin Doha na kasar Qatar da nufin tattauna hanyoyin samar da wani tsari na bai daya domin farfado da farashin man daya fadi warwars a kasuwancin duniya.
(last modified 2018-08-22T11:28:08+00:00 )
Apr 17, 2016 10:27 UTC
  • Ministan man fetir na Iran Bijan Namdar Zanganeh
    Ministan man fetir na Iran Bijan Namdar Zanganeh

Kasashe masu arzikin man fetir na duniya na halartar wani taro a birnin Doha na kasar Qatar da nufin tattauna hanyoyin samar da wani tsari na bai daya domin farfado da farashin man daya fadi warwars a kasuwancin duniya.

Taron dai nada nifin takaitawa ko dakatar da man da kasashen ke fitarwa, ko wala -alla firashin nasa zai farfado.

Saidai Iran wace ke daya daga cikin kassahen ta kauracewa taron saboda a cewar ta bashi da wata fa'ida a gare ta, domin ita bata da niyyar rage yawan man da take fitarwa, kamar yadda ministan man fetir din kasar Bijan Namdar Zanganeh ya sanar.

A nata bangare Saudiyya ta bakin yarima mai jiran gado Mohammed ben Salmane, ta bayyan a jiya Asabar cewa, Masarautar ba zata dakatar da fitar da dayan man ta ba, muddin Iran batayi hakan ba.