Mogherini: Gwajin Makamai Masu Linzamin Iran, Bai Saba Wa Yarjejeniyar Nukiliya Ba
(last modified Sat, 16 Apr 2016 17:43:51 GMT )
Apr 16, 2016 17:43 UTC
  • Mogherini: Gwajin Makamai Masu Linzamin Iran, Bai Saba Wa Yarjejeniyar Nukiliya Ba

Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta bayyana cewar gwajin makamai masu linzami da Iran ta yi a kwanakin baya bai saba wa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirin nukiliyanta na zaman lafiya ba.

Madam Mogherini ta bayyana hakan ne a yau din nan Asabar a wata ganawa da ta yi da manema labarai da takwaranta na Iran Dakta Muhammad Jawad Zarif a ci gaba da ziyarar da take a nan Iran inda yayin da take bayyana cewar Iran ta cika dukkanin alkawurran da ta dauka cikin yarjejeniyar nukiliya ta ce gwajin makamai masu linzami da Iran ta yi kwanakin baya bai saba wa yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma ba.

Jami'ar diplomasiyyar ta Turai ta bayyana cewar a halin yanzu dai an bude wani sabon shafi na alaka tsakanin Iran da kasashen Turai inda a yayin ziyarar tata bangarori biyun za su sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi na aiki a tsakaninsu don kara karfafa alakar da ke tsakanin bangarori biyu.

Maganar jami'ar diplomasiyyar ta Turai dai yana musanta zargin da jami'an Amurka suke ta yi ne na cewa gwajin makamai masu linzami da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar ta Iran suka yi a watannin baya ya saba wa kudurin kwamitin tsaro na MDD.

A yau ne dai Madam Moghrini ta iso nan Tehran don ganawa da manyan jami'an kasar da suka hada da takwararta Dakta Muhammad Jawad Zarif, shugaban majalisar Dakta Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar ta Iran Ali Shamkhani da sauransu don tattaunawa kan batutuwa daban-daban da suka shafi bangarori biyun.