Pars Today
Dauki ba dadi tsakanin 'yan sandan gwamnatin Jordan da wasu gungun 'yan ta'addan kasar ya lashe rayukan 'yan sanda akalla uku tare da jikkata wasu fiye da 20 na daban.
Jaridar Maariv ta haramtacciyar kasar Isra'ila ta ba da labarin cewa yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bn Salman yayi wata ganawa ta sirri da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, a birnin Amman na kasar Jordan.
Sarkin Jordan, Abdallah II, ya bukaci a yi wa dokar haraji wacce ta hadasa bore a kasar gyara.
Rahotanni daga Jordan, na cewa akwai yiwuwar masu bore su sake fitowa, duk da kiran da Sarkin kasar, Abdallah II, ya yi ga gwamnati akan ta soke shirin nan na karin kudadden man fetur da kuma na wutar lantarki.
Ministocin harkokin wajen kasashen Masar da Jordan sun yi Allah wadai da sojojin yahudawan mamaya na Isra'ila, bisa harbe wasu masu zanga-zanga lumana na Palasdinawa har lahira a zirin Gaza.
Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bukaci Kwamitin Kolin Kula da Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya da ya hanzarta bude bincike a Palasdinu.
Sarki Abdallah II na kasar Jordan ya gana da Fafaroma Francis inda suka tatattauna kan matsayin Birnin Kudus da kuma matakin da Amurka ta dauka na ayyanasa a matsayin babban birnin yahudawa sahayoniya 'yan mamaya.
Harin kunan bakin wake da aka kai sansanin 'yan ta'addan Jaishul-Islam da ke cikin kasar Siriya kusa da kan iyaka da kasar Jordan ya lashe rayukan mutane akalla 23 tare da jikkatan wasu 12 na daban.
Rahotanni daga Jordan na cewa wasu 'yan kasar biyu sun mutu, kana wani dan Isra'ila ya samu mummunan rauni a wani harin bindiga da aka kai a ofishin jakadancin HKI dake birnin Amman, a cikin daren jiya Lahadi.
A zaman da ministocin harkokin wajen kasashen da suka yanke alaka da Qatar wato Saudiya, Masar, UAE da kuma Bahrain suka gudanar a Masar a ranar Laraba da ta gabata, sun sanar da cewa ba su gamsu da amsar da Qatar ta ba su a kan bukatu 13 da suka mika mata ba.