Jordan : Sarki Abdallah Ya Gana Da Fafaroma Kan Kudus
Sarki Abdallah II na kasar Jordan ya gana da Fafaroma Francis inda suka tatattauna kan matsayin Birnin Kudus da kuma matakin da Amurka ta dauka na ayyanasa a matsayin babban birnin yahudawa sahayoniya 'yan mamaya.
Fadar Vatican ta ce shugabannin biyu sun tattauna ta fahimta kan tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da makomar Birnin da kuma mutunta addinai.
Fafaroman ya bukaci ci-gaba da mutunta matsayin Birnin Kudus kamar yadda ya ke a baya, yayin da Sarki Abdallah ya yi Alla-wadai da yadda shugaba Trump ya yi gaban kan sa wajen saba wa dokokin duniya.
ko baya ga hakan sarki Abdallah na Jordan ya kuma gana da shugaban kasar Faransa, Emanuelle Macron a Jiya kan batutuwa da dama ciki har da batun na Qudus.