An Kai Hari A Ofishin Jakadancin HKI Dake Amman
Rahotanni daga Jordan na cewa wasu 'yan kasar biyu sun mutu, kana wani dan Isra'ila ya samu mummunan rauni a wani harin bindiga da aka kai a ofishin jakadancin HKI dake birnin Amman, a cikin daren jiya Lahadi.
Majiyoyin tsaro daga Amman sun ce mutumin na farko mai suna Mohammed Jawawdeh dan shekara 17 ya rasa ransa nan take, yayin da na biyu mai suna Bashar Hamarneh wanda likita ne ya cika a asibiti.
Dan Isra'ilar da aka raunana shi ne mukadanshin darectan kula da sha'anin tsaro na ofishin jakadancin.
A ranar juma'a data gabata dubban mutanen Jordan ne suka gudanar da zanga-zanga Allah wadai da killacewa da kuma matakan da Isara'ila ke dauka a baya bayan nan a masallacin birnin Qudus.
Saidai labarin ya ce bai kai ga tantance ko harin na da alaka da hakan ko kuma A'a.