Sarkin Jordan Ya Bukaci A Yi Wa Dokar Haraji Gyara
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31456-sarkin_jordan_ya_bukaci_a_yi_wa_dokar_haraji_gyara
Sarkin Jordan, Abdallah II, ya bukaci a yi wa dokar haraji wacce ta hadasa bore a kasar gyara.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 05, 2018 13:47 UTC
  • Sarkin Jordan Ya Bukaci A Yi Wa Dokar Haraji Gyara

Sarkin Jordan, Abdallah II, ya bukaci a yi wa dokar haraji wacce ta hadasa bore a kasar gyara.

Duk da murabus din da Fira ministan kasar ya yi, dubban mutanen kasar ne ke ci gaba da zanga zanga yin tir da sabuwar dokar harajin gwamnatin da kuma la'antar asusun bada lamani na IMF wanda suka ce shi ne ke tura wamnatin ga daukar wannan shawara. 

Kungiyoyin kwadago a kasar sun ce kiran shugaban kasar alama ce mai kyau, amma dai sun yi kiran yajin aiki a gobe Laraba.

Bayanai daga kasar sun ce ana shirin gudanar da wata sabuwar zanga zanga da yammacin yau Talata, bayan buda baki.

Yau dai kusan mako guda da al'ummar ta Jordan ke zanga zanga kan dokar data kunshi karin kundin haraji, a wasu fannoni