-
Nijar : Hama Amadu Ya Rasa Mukaminsa Na Dan Majalisa
Jun 21, 2018 05:54Jagoran 'yan adawa na Nijar, kana shugaban jam'iyyar Moden Lumana, Hama Amadu, ya rasa mukaminsa na dan majalisar dokoki.
-
Gwamnatin Kongo Ta Ce Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Da Kotun ICC Ta Sake Yana Iya Dawowa Gida
Jun 19, 2018 05:49Gwamnatin kasar Demokradiyyar Kongo ta sanar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, Jean-Pierre Bemba, da kotun duniya mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) ta wanke na iya komawa gida, sai dai ba ta ce ko za a hukunta shi a kasar idan ya dawo ba.
-
Kotun ICC Ta Ba Da Umurnin Sake Tsohon Mataimakin Shugaban Kongo, Jean Pierre Bemba
Jun 13, 2018 05:29Alkalan kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffuka ICC sun ba da umurnin a sake tsohon mataimakin shugaban kasar Kongo kana kuma tsohon magudun 'yan tawayen kasar Jean-Pierre Bemba daga inda ake tsare da shi bayan bangaren daukaka kara na kotun ya wanke shi daga zargin aikata laifuffukan yaki da cin zarafin bil'adama da ake masa.
-
Kotun ICC Ta Wanke Tsohon Mataimakin Shugaban Kongo Daga Zargin Laifuffukan Yaki
Jun 09, 2018 10:42Kotun hukunta manyan laifufuka ta ICC da ke birnin Hague ta wanke tsohon mataimakin shugaban kasar Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo kana kuma tsohon madugun 'yan tawayen kasar, Jean-Pierre Bemba, daga tuhumar da aka masa na tafka laifukan yaki da cin zarafin bil'adama.
-
Kotu A Kaduna Ta Turo Tsohon Gwamnan Jihar, Yero, Gidan Yari
May 31, 2018 15:59Wata babbar kotun tarayya a Kaduna, da ke arewacin Nijeriya ta ba da umurnin a tsare tsohon gwamnan jihar Mukhtar Ramalan Yero da wasu mutane uku a gidan yari saboda zargin cin amana da halatta kudin haram.
-
Kotu Ta Zargi Shugabanin Yankunan Dake Amfani Da Inglishi Da Ta'addanci A Kamaru
May 26, 2018 11:04Wata kotu a kasar Kamaru ta yanke hukunci daurin shekaru 15 a gidan Kaso kan wasu shugabani na yankin dake amfani da turancin inglishi bisa laifin ta'addanci a kasar
-
Palasdinu Ta Bukaci ICC Ta Binciki Isra'ila Kan Laifukan Yaki
May 23, 2018 05:50Ministan harkokin wajen Palasdinu, Riyad al-Maliki, ya bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, data bude binciken gaggawa kan laifukan yaki da wariyar launin fata da ake zargin aikata wa kan Palasdinawa.
-
Kotu Ta Bukaci Firayi Ministan Gabon Ya Sauka Kuma A Rusa Majalisa
May 01, 2018 05:25Kotun tsarin mulki ta kasar Gabon ta ba da umurnin firayi ministan da yayi murabus daga mukaminsa sannan kuma a rusa karamar majalisar kasar bayan da aka jinkirta zaban 'yan majalisar da ya kamata a gabatar a makon da ya wuce.
-
ICC Ta Sake Watsi Da Bukatar Belin Laurent Gbagbo
Apr 24, 2018 11:05Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta sake yin watsi da bukatar bada belin tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo.
-
An Gurfanar Da Tsohon Shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma A Gaban Kotu
Apr 06, 2018 09:40A yau Juma'a, tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gurfana a gaban babbar kotun birnin Durban saboda zargin da ake masa na cin hanci da rashawa kan wani ciniki na makamai da suka kai dala biliyan 2.5 da aka yi tun a shekarun 1990.