-
Kungiyar Ikhwan A Masar Na Goyon Bayan Masu Yajin Cin Abinci A Gidajen Kason Kasar
Jun 03, 2017 08:36A cikin wani bayani da ta fitar kungiyar Ikhwanul Muslimin ta kasar Masar ta bayyana goyon bayanta ga yajin cin abinci wanda wasu fursinonin siyasa yayan kungiyar suke yi a kurkukun Leemon- Al-Manyaa, wanda a yau ya kai kwanaki ukku kenan. Bayanin ya kara da cewa laifin jami'an tsaron kasar ne ya tunzura fursinonin kai ga daukar wannan matakin
-
Yan Siyasa Da Kungiyoyin Fararen Hula A Libiya Sun Bukaci Hukunta Kwamandan Rundunar Sojin Kasar
Jun 01, 2017 14:53Wasu kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasar Libiya sun bukaci daukan matakin hukunta kwamandan rundunar sojin kasar kan hadin kan da ya bai wa gwamnatin Masar wajen keta hurumin kasar ta Libiya.
-
Sudan Ta Hana Shigo Da Kayan Marmari Da Bisashe Daga Masar
May 31, 2017 07:43Sakamakon takun sakar da ke ci gaba da kara tsanata a tsakanin gwamnatocin Sudan da kuma Masar, gwamnatin Sudan ta sanar da hana shigo da kayan marmari da bisashe daga kasar Masar.
-
Algeria Ta Bukaci Masar Ta Dakatar Da Hare Hare Kan Gabacin Kasar Libya
May 30, 2017 10:38Gwamnatin kasar Algeria ta yi kira ga kasar masar da ta dakatar da kai hare hare a gabancin kasar Libya, don hakan ba zai warware matsalolin tsaron da kasar take fama da su ba.
-
Gwamnatin Masar Ta Rattaba Hannu Kan Dokar Rage Walwalar Kungiyoyi Masu Zaman Kansu A Kasar
May 30, 2017 02:26Shugaban kasar Masar ya rattaba hannu kan sabuwar dokar da ta rage walwalar kungiyoyi masu zaman kansu a kasar.
-
Ministan Harakokin Wajen Rasha Ya Kai Ziyara Birnin Alkahira
May 29, 2017 13:48Yaki Da Ta'addanci Shi Ne Musababin Ganawar Magabatan Rasha Da Masar A birnin Alkahira
-
Masar A Shirye Take Ta Kaddamar da Hari A Kan 'Yan Ta'adda A Cikin Sudan
May 29, 2017 08:01Wani babban jami'in gwamnatin kasar Masar ya sheda cewa, kasarsa a shirye take ta kaddamar da hare-hare a kan wuraren buyar 'yan ta'adda a cikin Sudan, matukar bukatar hakan ta taso.
-
Gwamnatin Masar Ta Sanya Sunan Shugaban Kungiyar 'Ikhwan' Cikin Jerin 'Yan Ta'adda
May 29, 2017 01:17Gwamnatin kasar Masar ta sanya sunan shugaban kungiyar 'Muslim Brotherhood' ta kasar Muhammad Badie tare da wasu jagororin kungiyar cikin jerin sunayen 'yan ta'adda na kasar.
-
Rundunar Tsaron Masar Ta Tsaurara Matakan tsaro A Kan Iyakar Kasarta
May 28, 2017 14:45Rundunar tsaron Masar ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakar kasarta da kasashen Libiya da Sudan.
-
Jiragen Saman Yakin Masar Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanin 'Yan Ta'addan A Kasar Libiya
May 28, 2017 00:57Jiragen saman yakin rundunar sojin Masar sun kai farmaki kan sansanonin 'yan ta'adda a garin Derna da ke arewa maso gabashin kasar Libiya a matsayin maida martani kan harin ta'addancin da aka kai kan mabiya addinin Kirista a lardin Minya da ke kudancin kasar Masar, inda harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 29 tare da jikkata wasu adadi mai yawa.