Rundunar Tsaron Masar Ta Tsaurara Matakan tsaro A Kan Iyakar Kasarta
May 28, 2017 14:45 UTC
Rundunar tsaron Masar ta tsaurara matakan tsaro a kan iyakar kasarta da kasashen Libiya da Sudan.
Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar da kasashen da suke makobtanta da Masar da suka hada da Libiya da Sudan, inda jami'an tsaron kasar ta Masar suke gudanar da sintiri ta sama da kasa da nufin hana kutsen 'yan ta'adda zuwa cikin kasar.
Majiyar tsaron ta kara da cewa: Jiragen saman yakin Masar a shirye suke su ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin 'yan ta'adda da suke cikin kasar Libiya kamar yadda suka kai kan sansanin 'yan ta'addan a garin Derna na Libiya.
Tags