Sudan Ta Hana Shigo Da Kayan Marmari Da Bisashe Daga Masar
May 31, 2017 07:43 UTC
Sakamakon takun sakar da ke ci gaba da kara tsanata a tsakanin gwamnatocin Sudan da kuma Masar, gwamnatin Sudan ta sanar da hana shigo da kayan marmari da bisashe daga kasar Masar.
Jaridar Al-quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Firayi ministan kasar Sudan Bakri Hassan saleh ya sanar a jiya cewa, sun hana shigo da kayan marmari da sauran kayan amfanin gona gami daga bisashe daga Masar.
Ya ce wannan mataki ya hada ta hanyar ruwa da kuma hanyoyi na kasa da suka hada iyakokin kasashen biyu, inda hakan zai bayar da dama ga 'yan kasuwar kasar su shigo daga irin wadannan kayayyaki daga wasu kasashen na daban maimakon kasar masar.
Tags