Ministan Harakokin Wajen Rasha Ya Kai Ziyara Birnin Alkahira
Yaki Da Ta'addanci Shi Ne Musababin Ganawar Magabatan Rasha Da Masar A birnin Alkahira
Kafar watsa labaran Alyaumul-Sabi'i ta kasar Masar ta habarta cewa a wannan Litinin wata Babbar tawaga daga kasar Rasha bisa jagorancin Ministan harakokin wajen Kasar Sergei Lavrov ta kai ziyara birnin Alkahira, jim kadan bayan shiga cikin kasar, tawagar ta gana da magabatan kasar Masar bisa jagorancin Ministan harakokin wajen kasar Sameh Shukri.
Rahotanni sun ce bayan tattaunawa kan yanayi da kuma rikicin da yankin gabas ta tsakiya ke ciki, magabatan kasashen biyu sun tattauna kan yaki da ta'addanci musaman ma kan ta'addancin baya bayan nan da aka kai a kasar ta Masar.
Idan ba a manta ba dai a ranar Juma'ar da ta gabata ce wasu 'yan ta'adda suka kai hari kan wasu jerin Bas Bas dauke da mabiya addinin Kirista a garin Almaniya inda suka kashe 29 tare da jikkata wasu 24 na daban daga cikin su.
Har ila yau Mista Lavrov ya gana da Ahmad Abu Gaiz Babban saktaren kungiyar kasashen Larabawa a birnin na Masar, to saidai ba a bayyana mas'alolin da bangarorin biyu suka tattauna kan sa ba.
Kuma ana sa ran Ministan harakokin wajen Rashan zai gana da Shugaba Abdul-fatah Alsese na kasar ta Masar, inda ake sa ran za su tattauna kan alakar siyasa, tattalin arziki, al'adu, yawon buda biyu da rikicin yankin gabas ta tsakiya.