Mar 29, 2016 05:06
Gwamnatin kasar Pakistan ta sanar da shirinta da dirar mikiya a kan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayin addini musamman a lardin Punjab bayan harin ta'addancin da aka kai wani wajen wasa a garin Lahore, babban birnin lardin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta ce jami'an tsaron kasar na ci gaba da farautar mutanen da suka kai harin.