Pakistan : Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 28
A kasar Pakistan ruwa sama tamakar da bakin kwarya da aka samu kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 28 kamar yadda mahukuntan wannna kasa suka sanar a jiya Lahadi.
Bayanai daga kasar dai sun nuna cewa akasarin wadanda lamarin ya rutsa dasu sun rasa rayukan su sanadin ruftawar gidaje.
Yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Balushistan dake kudu maso yamma inda mutane 17 suka mutu, sai kuma wasu shida a Pakhtunkhwa dake arewa maso yammaci, yayin da wasu biyar suka mutu a yankin kabilu kamar yadda hukumar kula da harkokin da suka shafi bala'i ta kasar ta sanar.
A wani labari na daban an ce wasu ma'aikatan tono gwal biyar sun mutu a ruftawar mahakar yankin, kuma har zuwa jiya Lahadi sama da ma'aikatan mahakar 30 ne suka makalle ba'a samu fitar da su ba.
Kasar pakistan na fuskantar irin wannan al'amari kusan ko wace shekara musamman a lokacin damuna, inda ko a shekarar 2010 ambaliya ruwa a sassan kasar ta yi sanadin mutuwar mutane 1,700.