Rouhani Ya Bukaci Pakistan Da Ta Dau Tsauraran Matakai Kan ‘Yan Ta’adda
Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani ya kirayi kasar Pakistan da ta dau tsauraran matakan da suka dace wajen fada da ‘yan ta’addan da suke ci gaba da yin barazana ga tsaron kasar Iran.
Shugaba Rouhani yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan inda ya ce bai kamata Iran da Pakistan su bar wasu ‘yan tsirarrun ‘yan ta’adda, wadanda suke a matsayin kayan aikin wasu kasashe, su cutar da dadaddiyar alakar dake tsakaninsu ba.
Yayin da yake ishara da harin ta’addancin baya-bayan nan da aka kai lardin Sistan and Baluchestan na kasar ta Iran, shugaba Rouhani ya ce Iran tana sane da sansanin ‘yan ta’addan da suka kawo wannan hari a cikin kasar Pakistan don haka ya ce Iran tana jiran ta ga matakin da gwamnatin Pakistan za ta dauka kan wannan lamari ne, yana mai cewa Iran a shirye take ta hada kai da Pakistan wajen ganin bayan wadannan ‘yan ta’addan.
A ranar 13 ga watan Fabrairun da ya gabata ne dai ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Jaishul Adl da ke da alaka da kungiyar Al-Qaida suka kai hari kan wata mota da take dauke da dakarun kare juyin musulunci na kasar ta Iran kusa da garuruwan Zahedan da Khash da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 27 da raunana wasu 13.