Pakistan : An Sanya Dokar Hana Fita Bayan Hari A Masallaci
Hukumomi a lardin Butmaïna dake arewa maso gabashin kasar Pakistan sun sanya dokar hana fita bayan harin da wani dan kunar bakin wake ya kai jiya a lokafin da ake sallar Juma'a.
kawo yanzu adaddin mutanen da suka rasa rayukan su a harin ya kai 30 bayan da wasu biyu suka cika a asibiti da sanyin safiyar wannan Asabar.
ko baya ga hakan akwai wasu mutane sama da 30 da suka raunana, kamar yadda mukadashin kantoman yankin M. Naveed Akbar ya tabbatarwa da kanfanin dilancin labarai na faransa AFP.
Mutanen yankin wanda 'yan kabilar kuma Mohmand, ne sun ce akasarin wadanda suka mutun yara ne.
Tuni dai kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin a kauyen na Butmaïna dake kan iyaka da kasar Afganistan inda sojojin kasar ke yaki da kungiyar ta Taliban.
tunda farko dai mahukunatan yankin sun ce mutane 28 ne suka riga mu gidan gaskia kana wasu 30 suka raunana a yayin da kunar bakin waken ya tayar da boma-boman da yayi damara dasu a daidai lokacin da ake gudanar da sallar Juma'a a jiya.