Pakistan : Ruwan Sama Sun kashe Mutane 36
Rahotanni daga Pakistan na cewa mutane 36 suka rasa rayukan su kana wasu 27 na daban suka raunana sakamakon ruftawar gidajen su bayan wasu ruwa sama da aka samu tamakar da bakin kwarya.
Al'amurin dai ya faru ne da yammacin jiya Asabar a yankin arewa maso yammacin kasar
Alkalumen da hukumomin yankin suka fitar sun nuna cewa gidaje kimanin 40 ne suka rufta a wurare daban-daban a yankin Khyber Pakhtunkhwa.
Wannan adadin a cewar hukumar kula da iftila'i ta kasar zai iya karuwa kasancewar wasu wuraren da lamarin ya fasha nada wahalar shiga, wanda mafi yawan su ke akan tsaunuka.
Lamarin dai yafi kamari a yankunan Kohistan inda mutane 12 suka mutu, sai kuma Shanglas inda ruwan sama da zabtarewar kasa ya abkama inda aka samu hasara rayukan mutane kimanin goma.
Kusan dai a ko wace shekara akan fuskanci ire-iren wadanan iftila'i a Pakistan inda ko a bara mutane 81 suka rasa rayukan su a wata ambaliya da ruwan sama data shafi mutane 300,000 a fadin kasar.