Pakistan : Bam Ya Kashe Mutane 15 A Cikin Wata Bas
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i2500-pakistan_bam_ya_kashe_mutane_15_a_cikin_wata_bas
Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa mutane 15 suka rasa rayukan su biyo bayan fashewar wani bam a cikin wata matar bas.
(last modified 2018-08-22T11:27:59+00:00 )
Mar 16, 2016 12:21 UTC
  • Pakistan : Bam Ya Kashe Mutane 15 A Cikin Wata Bas

Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa mutane 15 suka rasa rayukan su biyo bayan fashewar wani bam a cikin wata matar bas.

bayanai sun nuna cewa mafi akasarin mutanen dake cikin bas din ma'aikatan gwamnati ne na birnin Peshawar dake kusa da iyaka da Afganistan.

ko baya ga mutanen da suka rasun an samu wasu 24 da suka raunana a tashin bam din da a cewar wasu rahotanni aka dana a bus din mai daukeda mutane akalla 50.