Pars Today
A wani abu da ake kallonsa a matsayin sassauci a rikici diflomatsiya na tsakanin kasahen Qatar da Saudiyya, sarki Salman ya bada umurnin bude iyakar kasashen biyu.
Tun bayan da kasashen Saudiyya, UAE, Bahrain da kuma Masar suka sanar da kakaba takunkumi a kan kasar Qatar, kasar Kuwait take ta kai gwabro ta kai mari domin ganin ta shiga tsakanin wadannan kasashe domin sulhunta su.
Hukumomin Qatar sun zargi Saudiyya da saka siyasa a cikin harkokin addini lamarin dake kawo cikas ga aikin hajji.
Kasar Saudiyya da kawayenta larabawa sun amai sun lashe dangane da jerin bukatun da suka gindayawa kasar Qatar kafin su maido da hulda da ita.
Ma'aikatar tsaron kasar Katar ta sanar da cewa Pakistan ta aike da jiragen sama samfurin Super Moshak na bada horo.
Jakadiyar kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa A MDD ta ce idan har kasar ta Katar din ba ta karbi sabbin sharuddan da aka kafa ma ta ba to za a korarta daga kungiyar larabawan yankin tekun pasha.
Saudiyya da kawayenta Larabawa sun ce yarjejeniyar yaki da ta'addanci da Amurka da Qatar suka cimma ''Bata Gamsar da su ba".
Ministan Harkokin Wajen kasar Katar Muhammad Abdurrahman ali-Sani ya fadawa tashar telbijin din Faransa cewa; Babu wani rikici wanda sai an yi amfani da karfi za a magance shi.
Kasar Qatar ta sanar da kafa wani kwamiti da zai bukaci kasashen larabawa abokan gabarta da su biya ta diyya bayan maida ta saniyar ware na tsawan makwanni biyar a yanzu.
Shugaban cibiyar kare hakkokin mutanen da ake zalunta a kasar Tunusiya ya jaddada yin kira ga kasashen da suka kakaba takunkumi kan kasar Qatar da cewa: Dole ne su kawo karshen takunkumin tare da maida hankali kan dambaruwar siyasar da take faruwa a cikin kasashensu.