Saudiyya Da Kawayenta Sun Yi Amai Sun Lashe Game Da Qatar
(last modified Thu, 20 Jul 2017 17:32:45 GMT )
Jul 20, 2017 17:32 UTC
  • Saudiyya Da Kawayenta Sun Yi Amai Sun Lashe Game Da Qatar

Kasar Saudiyya da kawayenta larabawa sun amai sun lashe dangane da jerin bukatun da suka gindayawa kasar Qatar kafin su maido da hulda da ita.

A ranar 4 ga watan Yulin nan ne dai kasashen da suka hada da Saudiyyar da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar a daya bangare suka gindayawa kasar ta Qatar jerin bukatu 13 kafin maido da alaka da ita, jerin bukatun da Qatar din ta yi watsi da su.

Bayan dai ja in ja na wani dan lokaci da kuma shiga tsakani na wasu kasashe ciki har da na yamma, abokan gabar na Qatar sun janye wasu daga cikin jerin bukatun 13, inda a yanzu suka janye batutuwan da suka hada da rufe tashar talabijin ta Aljazeera da kuma na rage hulda da Iran.

A halin da ake ciki dai kasahen sun gabatarwa da Qatar wasu jerin sabbin bukatu shida.

Daga cikinsu kuwa da akwai : 

1. Qatar ta dauki matakin yaki da tsatsauran ra'ayi da kuma ta'addanci na ko wanne irin hali.

2. Da Dakatar da duk wasu ayyuka na tsokana da kalamai na tada fitina.

3. Ta kuma mutunta yarjejeniyar Riyad ta 2013 data tanadi hadin gwiwa na kasashen yakin golfe.

4. Sannan ta yi na'am da sakamakon da taron Amurka da wasu kasashen musulmi dana larabawa ya cimma a watan Mayu da ya gabana a Riyad.

5. Ta kuma dakatar da tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasashen da kuma taimakawa wasu kungigoyi da basa bisa ka'ida

6. Sannan ta dauki yaunishiga cikin jerin kasahen duniya wajen bayyana ayyukan ayyukan ta'addanci da tsatsauran ra'ayi a matsayun babbar barazana ga tsaro da zamen lafiya a duniya. 

A yanzu dai ma'aikatar harkokin Saudiyya ta ce ita da kawayenta ba zasu zama teburin tattaunawa da Qatar ba har sai ta amunce da wadanan sabbin jerin bukatu shida.