Katar Ta Gargadi Saudiyya Akan Kai Mata Harin Soja
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i22078-katar_ta_gargadi_saudiyya_akan_kai_mata_harin_soja
Ministan Harkokin Wajen kasar Katar Muhammad Abdurrahman ali-Sani ya fadawa tashar telbijin din Faransa cewa; Babu wani rikici wanda sai an yi amfani da karfi za a magance shi.
(last modified 2018-08-22T11:30:22+00:00 )
Jul 10, 2017 19:10 UTC
  • Katar Ta Gargadi Saudiyya Akan Kai Mata Harin Soja

Ministan Harkokin Wajen kasar Katar Muhammad Abdurrahman ali-Sani ya fadawa tashar telbijin din Faransa cewa; Babu wani rikici wanda sai an yi amfani da karfi za a magance shi.

Ministan Harkokin Wajen kasar Katar Muhammad Abdurrahman ali-Sani ya fadawa tashar telbijin din Faransa cewa; Babu wani rikici wanda sai an yi amfani da karfi za a magance shi.

Ali Sani ya ci gaba da cewa Wajibi ne a zauna kan teburin tattaunawa kuma ya kamata ace Saudiyya ta fahimci cewa yin amfani da karfi zai jefa yankin cikin matsala mai girma.

Bugu da kari ministan harkokin wajen Katar din ya kara da cewa; Babu yadda za a yi kasarsa ta mika kai ga bukatun da su ka saba dokokin kasa da kasa.