Sharhi: Takunkumin Kawancen Saudiyyah Domin Durkusar Da Qatar
Tun bayan da kasashen Saudiyya, UAE, Bahrain da kuma Masar suka sanar da kakaba takunkumi a kan kasar Qatar, kasar Kuwait take ta kai gwabro ta kai mari domin ganin ta shiga tsakanin wadannan kasashe domin sulhunta su.
Wannan kawance na kasashen larabawa hudu da saudiyya ta kafa kuma take jagoranta domin durkusar da kasar Qatar, ya kakaba takunkumai masu tsanani a kan kasar ta Qatar da nufin tilasta ta zama mai mika wuya ga sharuddan da suka gindaya mata, lamarin da ya saka kasar ta kasar ta Qatar a cikin mawuyacin halin, musamman ma ganin cewa kasashen Saudiyya da UAE da suke makwabtaka da ita sun rufe dukkanin iyakokinsu da ita na sama da kasa da kuma, wanda kuma ta wadannan hanyoyin ne ake shigar mata kayan abinci da sauran kayan bukatar rayuwa, wanda hakan ya sanya kasar Iran ta bude dukkanin hanyoyinta sama da ruwa ga kasar ta Qatar, tare da shigar mata da dukkanin kayayyakin da take bukata na abinci da sauran kayan bukatar rayuwa, kamar yadda gwamnatin Turkiya wadda take dasawa da kasar ta Qatar, take shigar mata da wasu kayan abinci, inda a halin yanzu Iran da Turkiya ne suke baiwa Qatar dukkanin kayyaykin bukatuwa na yau da kullum.
Kasar Kuwait wadda daya ce daga cikin kasashe mambobi na kungiyar larabawan yankin Tekun Fasha, tun a farkon rikicin Qatar da kawancen Saudiyyah, ta fara fara tuntubar dukkanin bangarori, amma dai hakan bai iya kawo karshen rikicin da ke tsakanin wadannan kasashe ba, duk kuwa da cewa Amurka da sauran kasashen turai da suka hada da Jamus, Birtaniya da kuma Faransa, sun nuna goyon bayansu ga yunkurin da kasar ta Kuwai take yi, amma kuma a lokaci guda babu wani abin da suka yi na matsala lamba a kan sauran kasashen hudu da suka kakaba wa Qatar takunkumi kan su janye hakan, duk kuwa da cewa suna da damar da za su iya yin hakan.
Bayan kasa samun nasara a yunkurin da Kuwait ta yi tun daga farkon rikcin, a ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin kasar ta Kuwait ta fara wani sabon yunkurin na daban, da nufin ganin an samu daidaito tsakanin wadannan kasashen larabawa da suke zaman doya da manja, inda mataimakin firayi ministan kasar ta Kuwai Muhammad Abdullah Mubar Al-Sabah ya fara wani rangadi, a tsakanin Doha, Abu Dhabi da kuma Maskat, da nufin gabatar da sabbin shawarwari ga bangarorin rikicin.
To sai dai abin da masu bin diddigin lamarin suke shakku a kansa shi ne, ko a wannan karon Kuwait za ta iya yin nasara? abin da ake ganin kamar da wuya, musamman ganin yadda a cikin 'yan kwanakin nan, wasu daga cikin manyan jami'ai na masarautar Saudiyya suke yin furuci da cewa, Kuwait tana karkata ne ga Qatar, maimakon ta bin sahun Saudiyyah wajen kakaba mata takunkumi, wanda hakan a cewarsu yana a matsayin butulci ne ga Saudiyya, wadda ta taka rawa wajen gayyato Amurka domin yaki da Saddam Hussain a lokacin da ya mamaye Kuwait a cikin shekara ta 1990, inda Saudiyya ta kashe biliyoyin kan hakan.
A cikin wata makala da wani marubuci dan kasar Saudiyya Abdulrahman Rashin ya rubuta a cikin jaridar Sharq Al-ausat da ke kare manufofin gwamnatin Saudiyyah, ya bayyana cewa Kuwait ta manta irin zagon kasa da Qatar ta yi ta kulla mata, a lokacin da Saddam Hussain ya mamaye mata kasa, inda Qatar ce kasa daya tilo daga cikin kasashen larabawan yankin tekun fasha da taki amincewa da a fitar da kudiri a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, domin shelanta yaki a kan Saddam a karkashin inuwar majalisar dinkin duniya, inda yarima mai jiran gado na kasar Qatar a lokacin Hamad bin Khalifa ya ce ba za su goyi bayan a taimaka ma Kuwait a kan mamayar da Saddam Hussain ya yi mata ba, har sai Bahrain ta mika wa Qatar wasu tsibirai da suke takaddama a kan mallakarsu.
Da dama daga cikin masana suna kallon wannan furuci wanda marubuci da ke kare manuofin gwamnatin Saudiyya ya yi, a matsayin wata alama da ke nuna rashin gamsuwar Saudiyya da matakin da Kuwait ta dauka tun daga farkon wannan rikici, kuma ga alama hakan yana a matsayin wata ishara ga Kuwait a kan cewa, ko dai ta bi sahun kasashe masu hankoron gurgunta Qatar, ko kuma ita ma ta saurari nata lokacin.