Pakistan Ta Aike Da Jiragen Bada Horo Zuwa kasar Katar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22416-pakistan_ta_aike_da_jiragen_bada_horo_zuwa_kasar_katar
Ma'aikatar tsaron kasar Katar ta sanar da cewa Pakistan ta aike da jiragen sama samfurin Super Moshak na bada horo.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Jul 20, 2017 12:39 UTC
  • Pakistan Ta Aike Da  Jiragen Bada Horo  Zuwa kasar Katar

Ma'aikatar tsaron kasar Katar ta sanar da cewa Pakistan ta aike da jiragen sama samfurin Super Moshak na bada horo.

Ma'aikatar tsaron kasar Katar ta sanar da cewa Pakistan ta aike da jiragen sama samfurin Super Moshak na bada horo.

Shugaban Makarantar jiragen sama na kasar Katar Salam Hamad Akil al-Nabit ne ya sanar da hakan a jiya larabwa  sannan ya kara da cewa; Kasar Pakistan ta aike da jiragen bada horo na Supe Moshak domin kara wa matuka jiragen kasar kwarewa.

Kasar Katar ta sayi kayan yaki na fiye da dalar Amurka biliyan 10 da su ka ka hada da jiragen Apachi masu saukar angulu da makamai masu linzami samfurin patriot da kuma jiragen yaki.