-
Sojojin Rasha Sun Yi Nasarar Hana 'Yan Ta'adda Yin Amfani Da Makamai Masu Guba A Siriya
Mar 20, 2018 19:10Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa: Sojojin Rasha sun yi nasarar murkushe bakar aniyar 'yan ta'adda na kokarin yin amfani da makamai masu guba a kasar Siriya.
-
Sharhi: Putin Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Rasha Da Tazara Mai Yawa
Mar 19, 2018 06:38A jiya ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Rasha, wanda sakamakon zaben ya yi nuni da cewa shugaba Vladimir Putin mai ci ne ya lashe shi da tazara mai nisan gaske tsakaninsa da sauran abokan hamayyarsa 7, bayan da aka sanar da sakamakon mafi yawan mazabu, wanda a jimilla Putin ya samu kashi 76.6 cikin dari.
-
Rasha : Putin Ya Lashe Zabe Da Gagarimin Rinjaye
Mar 19, 2018 06:24Shugaba Vladimir Putin ya sake lashe zaben shugabancin kasar Rasha a karo na hudu, wanda zai bashi damar ci gaba da shugabancin kasar a wani wa'adi na shekaru shida masu zuwa.
-
An Fara Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Kasar Rasha
Mar 18, 2018 16:14Miliyoyin al'ummar kasar Rasha ne suka fito don kada kuri'arsu a zaben shugaban kasar da aka fara a yau din nan a zaben da ake ganin shugaban kasar mai ci Vladimir Putin ne zai lashe shi.
-
Rasha: Kasashen Turai Sun Shirya Wasan Kwaikwayon Makamai Masu Guba Domin Kai Wa Syria Hari
Mar 17, 2018 19:27Kakakin rundunar sojin kasar Rasha ya bayyana abin da yakira wasan kwaikwayo kan makamai masu guba a Syria da cewa shiri ne na kasashen turai, domin yin amfani da hakan wajen samun hujjar kai wa kasar Syria hari.
-
Amurka Ta Kakaba Wa Rasha Takunkumi Saboda Kutse A Zabenta na 2016
Mar 15, 2018 18:02Amurka ta sanar da sabbin takunkumi kan kasar Rasha, saboda a cewarta yi mata kuste a zaben shugaban kasa na 2016 da ya gabata.
-
Rasha Ta Ce Ita Ma Za Ta Kori Wasu Jami'an Diplomasiyyar Birtaniyya Daga Kasar
Mar 15, 2018 11:20Kasar Rasha ta ce nan ba da jimawa ba ita ma za ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Birtaniyya da suke kasar a matsayin mayar da martani ga korar jami'an diplomasiyyarta su 23 da Birtaniyya ta yi biyo bayan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu dangane da batun amfani da gubar da aka yi a kan wani tsohon dan leken asirin Rashan a birnin London.
-
Rasha Ta Gargadi Birtaniya Kan Ta Guji Neman Yin Fito Na Fito Da Ita
Mar 15, 2018 05:39Ma'aikatar harkokin wajen kasar rasha ta sanar da cewa, Birtaniya ta zabi bin hanyar dagula lamurra a tsakaninta da Rasha, ta hanyar tuhumar Rasha da kashe tsohon jami'in leken asirinta.
-
Rasha Ta Ja Kunnen Birtaniyya Da Ta Sake Tunani Kafin Kawo Mata Harin Ta Yanar Gizo
Mar 14, 2018 11:06Kasar Rasha ta ja kunnen gwamnatin Birtaniyya da ta sake tunani sosai kafin ta aiwatar da barazanar kai mata hare-hare ta yanar gizo biyo bayan zargin da Birtaniyyan take yi wa Rashan na hannu cikin kokarin kisan gillan da aka yi wa wani tsohon dan leken asirin kasar a London a kwanakin baya ta hanyar amfani da guba.
-
Rasha Ta Ce Za Ta Mayar Da Martani Idan Amurka Ta Kai Hari Siriya
Mar 13, 2018 11:17Wani babban jami'in sojin kasar Rasha ya bayyana cewar sojojin Rashan za su mayar da martani ga duk wani harin da sojojin Amurka za su kai kasar Siriya matukar dai harin ya zamanto barazana ga rayuwar sojojin Rashan da suke Siriya.