Rasha : Putin Ya Lashe Zabe Da Gagarimin Rinjaye
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29203-rasha_putin_ya_lashe_zabe_da_gagarimin_rinjaye
Shugaba Vladimir Putin ya sake lashe zaben shugabancin kasar Rasha a karo na hudu, wanda zai bashi damar ci gaba da shugabancin kasar a wani wa'adi na shekaru shida masu zuwa.
(last modified 2018-08-22T11:31:34+00:00 )
Mar 19, 2018 06:24 UTC
  • Rasha : Putin Ya Lashe Zabe Da Gagarimin Rinjaye

Shugaba Vladimir Putin ya sake lashe zaben shugabancin kasar Rasha a karo na hudu, wanda zai bashi damar ci gaba da shugabancin kasar a wani wa'adi na shekaru shida masu zuwa.

Kwarya kwarya kidayar kuri'un zaben da aka yi a kashi 85% ya nuna cewa, shugaba Putin ya samu sama da kashi 76% na yawan kuri'un.

Dan takara jam'iyyar kwaminis ne Pavel Groudinine, ke biye masa da 12,1%.

Hukumar zaben kasar ta (CEC) ta ce an samu fitowar jama'a da 60%.

Saidai 'yan adawa a kasar sun ce an tafka kura-kurai masu yawa a zaben.

A jiya Lahadi ne al'ummar kasar ta Rasha suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar.