Mar 15, 2018 05:39 UTC
  • Rasha Ta Gargadi Birtaniya Kan Ta Guji Neman Yin Fito Na Fito Da Ita

Ma'aikatar harkokin wajen kasar rasha ta sanar da cewa, Birtaniya ta zabi bin hanyar dagula lamurra a tsakaninta da Rasha, ta hanyar tuhumar Rasha da kashe tsohon jami'in leken asirinta.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa; a cikin bayanin da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta fitar a jiya Laraba, ta bayyana cewa dukkanin zargin da Birtaniya take yi bai ginu a kan wani dalili ko hujja ba, illa dai kawai hakan yana a matsayin wani makami ne da Birtaniya take son yin amfani da shi domin cimma wasu manufofinta na siyasa a kan Rasha.

Bayanin ya ce yana da kyau Birtaniya ta yi taka tsatsan wajen neman yin fito na fito da kasa kamar Rasha, domin hakan ba zai haifar da da mai ido ba.

Dangane da wa'adin ficewa daga kasarta a cikin mako guda da Birtaniya ta baiwa wasu jami'an diflomasiyyar Rasha guda 23 kuwa, Rasha ta ce za ta mayar da martanin da ya dace a kan lamarin.

Tags