Mar 14, 2018 11:06 UTC
  • Rasha Ta Ja Kunnen Birtaniyya Da Ta Sake Tunani Kafin Kawo Mata Harin Ta Yanar Gizo

Kasar Rasha ta ja kunnen gwamnatin Birtaniyya da ta sake tunani sosai kafin ta aiwatar da barazanar kai mata hare-hare ta yanar gizo biyo bayan zargin da Birtaniyyan take yi wa Rashan na hannu cikin kokarin kisan gillan da aka yi wa wani tsohon dan leken asirin kasar a London a kwanakin baya ta hanyar amfani da guba.

Firayi ministan kasar Birtaniyyan Theresa May ce dai ta zargin gwamnatin Rashan da harin da aka kai wa Sergei Skripal da 'yarsa da wani sinadari mai guba da aka kirkiro shi a zamanin tsohuwar Tarayyar Sobiyeti, a birnin London inda yake zaune tana mai ba wa gwamnatin Rashan wa'adin zuwa daren jiya da ba da amsa kan wannan zargin da ake mata ko kuma a dau matakan takunkumi da sauransu ciki kuwa har da kai hare-hare ta yanar gizo kasar Rashan.

Kasar Rasha dai ta yi watsi da wannan zargin da kuma jan kunnen Birtaniyyan da ta guji daukar wannan mataki da ta ce za ta dauka din don kuwa kasar Rasha ba kasa ce da za a mata irin wannan barazana din ba.

Ko a jiya ma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rashan Maria Zakharova ta yi watsi da wannan wa'adi na firayi ministan Birtaniyya tana mai cewa a halin yanzu kasar Rasha ta wuce a yi mata irin wadannan barazana.

 

Tags