Pars Today
A jiya Asabar 20, Mayun 2017 ne shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya a ziyararsa ta farko zuwa wata kasa ta waje tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar Amurkan.
Cikin wani bayyani da ta fitar majalisar Zartarwar Kungiyar Ansarullah ta Kasar Yemen ta dora alhakin mawuyacin halin da Al'ummar kasar ke ciki a kan kasar Saudiya da kwamitin tsaron MDD.
Kawo ya zuwa yanzu mutanen da su ka mutu a garin Awamiyya na mabiya shi'a sun kai hudu.
Sarkin Saudiya Salman bn Abdul-Aziz ya tura goron gayyana ga Shugabanin kasashen musulmi 17 domin su gana da Shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Riyad.
Kungiyar ta "Human Right Watch' ta ce; tarihin Saudiyya akan batun hakkin dan'adam ba shi da kyau, domin kuma tana azabtar da masu fafutuka.
Firayi ministan kasar Birtaniya Theresa May ta gana da sarkin kasar Saudiyya a yammacin jiya a fadar Yamama da ke birnin Riyad.
Rundunonin sojin saman kasashen Sudan da Saudiyya sun fara gudanar da wani atisayen soji na hadin gwiwa da nufin karfafa rundunar sojin saman kasashen biyu domin ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen.
Mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin jin kan bil-Adama ya sanar da cewa: Akalla kananan yara 1400 ne aka kashe sakamakon hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yamen.
A wani abu da dama suka fassara shi a matsayin wani wasan kwaikwayo, gwamnatin Saudiyya ta yi ikirarin cewa tana kan gaba wajen fada da ayyukan ta'addancin da a halin yanzu ya zamanto babban bala'i ga duniya.
Makami mai Lizzami da Sojojin Yemen suka halba zuwa wani sansanin soja dake yankin Almazahimiya a yammacin birnin Riyad, ya razana magabatan Saudiya