Sharhi:Saudiya Da MDD Na Kokarin Raba Kasar Yemen
Cikin wani bayyani da ta fitar majalisar Zartarwar Kungiyar Ansarullah ta Kasar Yemen ta dora alhakin mawuyacin halin da Al'ummar kasar ke ciki a kan kasar Saudiya da kwamitin tsaron MDD.
Majalisar zartarwar kungiyar Ansarullah ta ce manufar makiyan Yemen shi ne rarraba kasar bisa jagorancin tsohon shugaban kasar da ya yi murabus Abdu Rabahu Mansur Hadi,kuma a halin yanzu shi ne abinda yake zartarwa, Majalisar ta tabbatar da cewa magoya bayan Mansur Hadi daga cikin su har da MDD na jan lokaci tare kuma da kokarin daukan hankalin kungiyoyin kasa da kasa wajen shashanta tattaunawar siyasa da ake yi domin ceto kasar daga cikin mawuyacin halin da take ciki.
A nasa bangare Piraministan Gwamnatin ceton kasar ta Yemen ya sanar da cewa kudirin Kwamitin tsaron MDD a kan al'ummar Yemen, an samar da shi ne bisa makudan daloli da Saudiyar ta bayar cin hanci ga Kwamitin.
Abdul-aziz bn Jabtur ya ce daga shekarar 2015 zuwa yau kasar Saudiyar ke lugudar wuta tare da kai hare-hare irin na dabbanci kan Al'ummar kasar ta Yemen bisa cikekken goyon bayan wasu kasashen Larabawa musaman ma manboboin kwamitin kasashen tekun fasha.
Kasawar da MDD ta nuna wajen magance rikice-rikice kasa da kasa musaman dangane da rikicin gabas ta tsakiya a baya bayan nan akwai dora Ayar tambaya a cikinsa, kuma ya zama wajibi a gudanar da bincike kan hakan, Shakka babu tasirin da wasu manyan kasashe masu fada'a a MDD da kuma mumunar siyasar su shi ne ya janyo halin da kasar yemen ke cikin a yanzu misali barazanar da kasar Saudiya ke yi na janye tallafin da take bayar wa ga Majalisar ya sanya Majalisar yin gum da bakinta wajen kallon saudiya na ci gaban da kisan gilla kan Al'ummar yemen.baya ga hakan rashin bayar da kyakkyawar shawarar da za ta taimaka wajen magance rikicin yankin na daga cikin ababen da nuna kasawar siyasar MDD a yankin.
Ci gaba da ta'addancin Saudiya tare da kashe Al'ummar kasar Yemen musaman ma Mata da kananen yara na daga cikin sakacin da magabatan MDD suka yi dangane da kasar Saudiya, cire sunan Saudiya daga cikin jerin kasashen dake take hakin kananen yara a Duniya na daga cikin bayanannun hujjoji na kasawar MDD wajen warware rikicin kasar ta Yemen duk kuwa da irin Dubun dubatan yaran da ta yi sanadiyar shahadar su yayin da wasu kuma ta mayar da su masakai.
Wani abu da ya fi daukar hanakalin kungiyoyin kasa da kasa a nan shi ne yadda Majalisar Dinkin Duniyar bisa goyon bayan kasashen Yamma ta sanya kasar Saudiyar manba a Kwamitin kare hakin bil-adama na Majalisar duk da irin ta'addancin da kasar ke yi a kasar Yemen, wannan kuma na zuwa ne bayan zaben da ake yiwa Saudiya a kwamitin kare matsayin Mata na MDD, lamarin da ya fuskanci kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakin bil-adama na kasa da kasa.
Shakka babu matsayar da MDD ta dauka wani sako ne ga magabatan kasar Saudiya na su ci gaba da ta'addancin da suke yi a kasar Yemen, kuma idan aka diba mawuyacin halin da Al'ummar yemen ke ciki a yanzu, ana iya cewa magabatan masarautar Ali-Sa'iud da Majalisar Dinkin Duniya su suka janyo matsananciyar wunya, fari da kuma annobar da Al'ummar Yemen ke fuskanta a halin yanzu kuma wannan shi ne abinda magabatan kasar ta yemen suka tafi a kansa.